Honarabul Mikati ya Maka Isah Ashiru Kudan da Jam’iyyarsu ta ADC a Kotu

Daga Kallamu Galadima Dambo.   Honarabul Shu’aibu Idris Mikati, ya maka, Honarabul Isa Ashiru Kudan, da Jam’iyyarsu ta ADC, harma da Hukumar Zaɓe ta Najeriya (INEC) a gaban kotu.   Miqati ya garzaya gaban babbar kotun Taraiya da ke birnin Abuja ne bisa zargin yunkurin tauye masa hakkinsa, bayan samun nasarar lashe zaben fidda gwani […] The post Honarabul Mikati ya Maka Isah Ashiru Kudan da Jam’iyyarsu ta ADC a Kotu appeared first on GTR .

Honarabul Mikati ya Maka Isah Ashiru Kudan da Jam’iyyarsu ta ADC a Kotu












Daga Kallamu Galadima Dambo.

 

Honarabul Shu’aibu Idris Mikati, ya maka, Honarabul Isa Ashiru Kudan, da Jam’iyyarsu ta ADC, harma da Hukumar Zaɓe ta Najeriya (INEC) a gaban kotu.

 

Miqati ya garzaya gaban babbar kotun Taraiya da ke birnin Abuja ne bisa zargin yunkurin tauye masa hakkinsa, bayan samun nasarar lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar ADC, da aka gudanar kwanakin baya.

 

Zaɓen 2027 Fafatawa ce Tsakanin Talakawan Najeriya da Shugaba Tinubu – Musa Gebi

 

Zaben fidda gwanin dai ya nuna cewa, Idris Mikati, ne ya samu galaba kan abokanan karawarsa da suka fafata a masu neman ADC ta tsayar da su takarar gwamnan jihar Kaduna, kamar yadda aka sanar a sakamakon bincike da kwamitin bincike ya gudanar a kan zaben farko na fidda gwani da a kayi. Kwamitin sauraron korafe-korafe ya gano an yi magudi kuma ya bada sakamakon binciken da yayi ga shugabannin jamiyyar kusan watanni biyu da suka gabata.

 

Ya Kamata Gwamnan Kano ya Kai Ziyarar Ba Zata Asibitin AKTH, Musamman Bangaren Wankin Ƙoda – Salisu Abdul

 

Sai dai Kuma bayan da hukumar zaben Najeriya (INEC), ta rufe karbar sunayen ‘yan takara, rahotanni sun nuna cewa Jam’iyyar ADC ta tura sunan Isa Ashiru Kudan, a matsayin dantakarar Gwamnan jihar Kaduna maimakon Shu’aibu Idris Mikati, da tun da fari magoya bayansa ke cike da annashuwar samun nasara.

 

Honarabul Mikati ya Maka Isah Ashiru Kudan da Jam'iyyarsu ta ADC a Kotu

 

Wani Jigo a Jam’iyyar ADC da ya bukaci a sakaya sunansa ya shaidawa GTRHausa cewa akwai alamar tambaya kan sahihancin takardar da aka fitar, wadda ake ikirarin ta fito ne daga shelkwatar Jam’iyyar ADC dangane da sunayen ‘yan takarar.

 

Atiku ya Kai Tinubu Ƙara Kotu Kan Cancantarsa ta Tsayawa Takarar Zaɓen 2027

 

GTR Hausa ta yi kokarin jin ta bakin Honarabul Isa Ashiru Kudan da Kuma Lauyan jam’iyyar ADC, amma har lokacin hada wannan rahoton ba basu waiwaye mu ba duk da jinkirtawa da muka yi kafin fitar da wannan labari.

 

Abun jira a gani dai shi ne yadda za a kammala wannan Sa toka Sa Katsi, da ta kunno kai a tsakanin masu neman takarar Kujerar gwamnan jihar Kaduna a karkashin Jam’iyyar ADC.

 

Ku Guji Aikata Abubuwa Marasa Kyau a Ranar Takutaha – Malam Ibrahim Mai Ashafa

The post Honarabul Mikati ya Maka Isah Ashiru Kudan da Jam’iyyarsu ta ADC a Kotu appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow