H-JRBDA za ta Fara Gwajin Wutar Lantarkin da Aka Samar ta Hanyar Amfani da Tiga Dam

Daga Usman Hamza, Kano.   Hukumar raya kogunan Hadejia da Jama’are (H-JRBDA), ta ce za ta fara gwajin wutar lantarkin da aka samar ta hanyar amfani da ruwan Dam din Tiga.   Manajan Daraktan Hukumar, Injiniya Rabiu Sulaiman Bichi, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da Mataimakin Daraktan yada labaran Hukumar, Salisu […] The post H-JRBDA za ta Fara Gwajin Wutar Lantarkin da Aka Samar ta Hanyar Amfani da Tiga Dam appeared first on GTR .

H-JRBDA za ta Fara Gwajin Wutar Lantarkin da Aka Samar ta Hanyar Amfani da Tiga Dam

Daga Usman Hamza, Kano.

 

Hukumar raya kogunan Hadejia da Jama’are (H-JRBDA), ta ce za ta fara gwajin wutar lantarkin da aka samar ta hanyar amfani da ruwan Dam din Tiga.

 

Manajan Daraktan Hukumar, Injiniya Rabiu Sulaiman Bichi, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da Mataimakin Daraktan yada labaran Hukumar, Salisu Baba Hazmat ya fitar a daren jiya Jumu’a, inda ya ce an shirya fara gwajin tunkuda wutar daga Yau Asabar, 14 ga watan Maris na Shekarar 2026.

 

Jami’ar FUDMA ta Dakatar da Ɗalibai 20 Bisa Zarginsu da Satar Jarrabawa

 

Haka kuma ya ce fara gwajin tunkuda wutar lantarkin ba zai shafi manoma da sauran masu amfani da ruwan ba, adan haka su kwantar da hankalinsu.

 

Aikin samar da wutar Lantarkin mai ƙarfin Megawat 8, an yi shi ne da haɗin guiwar kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na jihar Kano (KEDCO)

 

Sakon Fadakarwa Daga Kamfanin GEZA AND SONS (Ashirin da Biyar ga Ramadan)

The post H-JRBDA za ta Fara Gwajin Wutar Lantarkin da Aka Samar ta Hanyar Amfani da Tiga Dam appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow