Gwamnatin Kano ta Rufe Makarantun Koyar da Aikin Lafiya Guda Biyu

Daga Bashir Gasau.   Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano, ta rufe wasu makarantu masu zaman kansu guda biyu da ke koyar da aikin lafiya.   Kakakin Ma’aikatar, Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa GTR Hausa a safiyar yau Talata, inda ya ce an ɗauki […] The post Gwamnatin Kano ta Rufe Makarantun Koyar da Aikin Lafiya Guda Biyu appeared first on GTR .

Gwamnatin Kano ta Rufe Makarantun Koyar da Aikin Lafiya Guda Biyu

Daga Bashir Gasau.

 

Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano, ta rufe wasu makarantu masu zaman kansu guda biyu da ke koyar da aikin lafiya.

 

Kakakin Ma’aikatar, Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa GTR Hausa a safiyar yau Talata, inda ya ce an ɗauki matakin ne a sakamakon yadda suke gudanar da aiyukansu ba tare da cika ƙa’idoji da sharuddan da suka dace ba a Ƙaramar Hukumar Nassarawa.

 

Dalilai Uku ne Suka Kara Ta’azzara Matsalar Tsaron Najeriya – Jabir Bichi

 

Makarantun da abin ya shafa sun haɗar da IBN SINA College of Health Science and Technology da ke Dakata Kawaji kusa da Babban Masallacin Juma’a, da kuma Life Line College of Health Science and Technology da ke rukunin masana’antu na Dakata, kan Titin zuwa Bela.

 

A cewar Nabilusi, “Matakin rufe makarantun ya biyo bayan bincike da tantancewa da Ma’aikatar Lafiya ta gudanar, inda aka gano cewa duka makarantun ba su cika sharudda da ƙa’idojin da aka gindaya domin kafa wa da gudanar da cibiyoyin koyar da aikin lafiya ba”.

 

Har Gobe Babu Mu Babu Sulhu da ‘Yan Bindiga – Gwamnatin Zamfara

 

Binciken ya nuna cewa makarantun ba su samu tantancewa da amincewa daga Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ba, haka kuma ba su da sahihin izini ko shaidar amincewa daga hukumomin da ke kula da harkokin koyar da ilimin lafiya a matakin ƙasa.

 

Sauran matsalolin da aka gano sun hadar da ƙarancin ƙwararrun malamai da ma’aikatan koyarwa, rashin wadatattun gine-gine da kayan aiki na koyarwa, tare da gaza cika ƙa’idojin ilimi da na gudanarwar da ake buƙata wajen horas da ƙwararrun ma’aikatan lafiya.

 

Bidiyo: Yadda Shugaban NDLEA na Najeriya ya Sha Ruwan Addu’oi a Tsangayar Alaramma Bagobiri

 

Bugu da ƙari, binciken ya bayyana rashin bin ƙa’idojin ɗabi’a da dokokin aiki na ƙwararru, da kuma wasu muhimman sharudda da aka tanada domin tabbatar da ingantaccen ilimin lafiya da samar da ma’aikatan lafiya masu ƙwarewa.

 

A karshe Ma’aikatar ta jaddada aniyarta na kare ɗalibai, iyaye da al’umma gaba ɗaya daga cibiyoyin da ke gudanar da aiyukansu ba bisa ƙa’ida ba, tare da tabbatar da cewa koyar da harkokin lafiya na gudana ne kawai a cibiyoyin da suka samu sahalewa kuma suka cika dukkan sharuddan da hukumomi suka tanada.

 

Akwai Buƙatar Musulmi da Kirista su Hada Hannu Wajen Koyar da Ilimin Addinansu a Makarantun Firamare da Sakandiren Arewacin Najeriya – Rabaran Kunama

The post Gwamnatin Kano ta Rufe Makarantun Koyar da Aikin Lafiya Guda Biyu appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow