FFS Gombe ta Horas da Jami’anta Kan Dabarun Ceto Waɗanda Iftila’i ya Shafa

Daga Aliyu Gerengi, Gombe.   Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya reshen Jihar Gombe, ta bawa Jami’anta horo kan amfani da “Mobile Life Jacket” domin inganta ceto a ruwa da kuma kare rayuka a yankunan dake fuskantar ambaliyar ruwa.     A jawabinsa, Kwamandan Hukumar na jihar Gombe, DCF SM Sulaiman, ya jaddada kudirinsa na ci-gaba […] The post FFS Gombe ta Horas da Jami’anta Kan Dabarun Ceto Waɗanda Iftila’i ya Shafa appeared first on GTR .

FFS Gombe ta Horas da Jami’anta Kan Dabarun Ceto Waɗanda Iftila’i ya Shafa

Daga Aliyu Gerengi, Gombe.

 

Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya reshen Jihar Gombe, ta bawa Jami’anta horo kan amfani da “Mobile Life Jacket” domin inganta ceto a ruwa da kuma kare rayuka a yankunan dake fuskantar ambaliyar ruwa.

 

FFS Gombe ta Horas da Jami'anta Kan Dabarun Ceto Waɗanda Iftila'i ya Shafa

 

A jawabinsa, Kwamandan Hukumar na jihar Gombe, DCF SM Sulaiman, ya jaddada kudirinsa na ci-gaba da inganta kwarewar jami’ansa domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

 

Shugaba Tinubu ya Naɗa, Bianca Odumegwu-Ojukwu, a Matsayin Ministar Harkokin Wajen Najeriya

 

An bada horon ne a ƙarkashin manufar sake horaswa ta Shugaban Hukumar na kasa, Olumode Samuel Adeyemi, inda Malam Salihu Mahmud, na SAFE RIVERINE Consultant Limited ya jagoranci bada bitar a jihar Gombe.

 

FFS Gombe ta Horas da Jami'anta Kan Dabarun Ceto Waɗanda Iftila'i ya Shafa

 

A ƙarshe sanarwar da Kakakin hukumar na jihar Gombe, ASF MB Muazu, ya aiko wa GTR Hausa ta ce Jami’an da suka halarci bitar, sun sami ilimi da atisayen amfani da kayan ceton rai domin kai ɗaukin gaggawa yadda ya kamata.

 

Gwamnatin Kano za ta yi Auren Gata na Mutane Dubu Uku

The post FFS Gombe ta Horas da Jami’anta Kan Dabarun Ceto Waɗanda Iftila’i ya Shafa appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow