Dattawa da Jami’an Tsaron Unguwar Tukuntawa Sun Dakile Fadan Daban da ya Taso

Daga Usman Hamza, Kano.   Dattawa da masu ba da shawara a unguwar Tukuntawa ta ƙaramar hukumar Birnin jihar Kano, sun daƙile fadan daban da ya yi shirin faruwa a yankin.   Tunda farko dai an shiga cikin yanayin tashin hankali a unguwar bayan wasu matasa daga unguwar Gandun Albasa, sun halarci wani ɗaurin aure […] The post Dattawa da Jami’an Tsaron Unguwar Tukuntawa Sun Dakile Fadan Daban da ya Taso appeared first on GTR .

Dattawa da Jami’an Tsaron Unguwar Tukuntawa Sun Dakile Fadan Daban da ya Taso

Daga Usman Hamza, Kano.

 

Dattawa da masu ba da shawara a unguwar Tukuntawa ta ƙaramar hukumar Birnin jihar Kano, sun daƙile fadan daban da ya yi shirin faruwa a yankin.

 

Tunda farko dai an shiga cikin yanayin tashin hankali a unguwar bayan wasu matasa daga unguwar Gandun Albasa, sun halarci wani ɗaurin aure inda aka shiga wani yanayi da ya kusa rikidewa zuwa fadan daba.

 

Matsalar da Najeriya ke Ciki Laifin Talakawan Ƙasar ne – Abdulkarimu Daiyabu

 

Mazauna yankin sun ce rikicin ya samo asali ne a sakamakon saɓani tsakanin wasu matasa, lamarin da ya haddasa firgici da ruɗani a tsakanin jama’a tare da tayar da hankalin mazauna yankin.

 

Mafari kenan da Dagacin Gandun Albasa ya yi gaggawar sanar da jami’an tsaro halin da ake ciki domin dakile rikicin tun kafin ya girmama, adan haka ne Baturen ‘yan sandan Sharada (DPO), Muhammad Adamu, ya tura jami’ansa zuwa wurin domin tabbatar da doka da oda tare da hana duk wani yunkuri na tayar da tarzoma.

 

NBA (Ungogo Branch) Kano ta Bukaci Shugaba Tinubu ya Magance Matsalar Tsaron Najeriya

 

Da yake yin karin haske kan lamarin, Dagacin Gandun Albasa, Injiniya Alkasim Yakubu, ya ja hankalin matasa da iyaye kan muhimmancin kiyaye zaman lafiya da kaucewa duk wani abu da zai haddasa rikici a tsakanin al’umma.

 

Ya bukaci iyaye su kara sanya ido kan tarbiyyar ‘ya’yansu, yayin da ya shawarci matasa da su rungumi mutunci, hakuri da zaman lafiya domin ci-gaban al’umma baki daya.

 

A karshe ya godewa dukkan wadanda suka taimaka wajen sasanta matasan cikin hikima, lamarin da ya taimaka matuƙa wajen dawo da zaman lafiyar yankin.

 

Jam’iyyar Action Alliance ce Jirgin Fiton Talakawan Najeriya – Ma’ajin Jam’iyyar na Kasa

The post Dattawa da Jami’an Tsaron Unguwar Tukuntawa Sun Dakile Fadan Daban da ya Taso appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow