Bai Kamata Malamai Su Dinga Kafurta Masu Yin Maulidi ba – Dan Azumi Gwarzo

Daga Bashir Gasau.   Tsohon Kwamishinan kasafi da tsare-tsare na jihar Kano, Honarabul Ibrahim Dan Azumi Gwarzo, ya ce bai kamata Malamai su rika Kafurtawa ko aibata masu yin Maulidi ba, gudun rarrabuwar kan musulmai.   Dan Azumi Gwarzo, ya baiyana hakan ne a yayin ganawarsa da manema Labarai a Kano, inda ya ce akwai […] The post Bai Kamata Malamai Su Dinga Kafurta Masu Yin Maulidi ba – Dan Azumi Gwarzo appeared first on GTR .

Bai Kamata Malamai Su Dinga Kafurta Masu Yin Maulidi ba – Dan Azumi Gwarzo












Daga Bashir Gasau.

 

Tsohon Kwamishinan kasafi da tsare-tsare na jihar Kano, Honarabul Ibrahim Dan Azumi Gwarzo, ya ce bai kamata Malamai su rika Kafurtawa ko aibata masu yin Maulidi ba, gudun rarrabuwar kan musulmai.

 

Dan Azumi Gwarzo, ya baiyana hakan ne a yayin ganawarsa da manema Labarai a Kano, inda ya ce akwai malaman da suke la’antar masu yin murna da watan da aka haifi fiyayyan halitta Annabi Muhammad (S A W), lamarin da ke kara raba Kawunan Musulmi.

 

Gwamnatin Jigawa da Kungiyar WOFAN Sun Ƙarfafa Haɗin Guiwa Kan Sauya Harkar Noma, Don Shigar da Mata da Matasa da Masu Bukata ta Musamman

 

Gwarzo wanda Tsohon Shugaban kwamitin Tasarrufi da rabon filayen jihar kano, ne ya kara da cewa bai dace da koyarwar addini ba, Malamai su rika hawa Mumbari suna furta kalmomin kafurta wadanda suke layin wata Darika, musamman masu yin murna da watan da aka haifi fiyayyan halitta.

 

Hotunan Makaman da Hukumomin Nijar Suka Ƙwace Daga Hannun Sojojin da Suka yi Bore

 

Ya kuma nuna muhimmancin Watan da ranar da akai haifi Manzon Allah (S A W), inda ya baiyana cewa babu wani Wata ko Ranar da tafi wannan daraja, hakan yasa wasu ke nuna farin cikin su ta hanyar shirya tarukan Maulidi musamman a Islamiyyu.

 

A karshe ya yi kira ga masu shirya tarukan Maulidin da su rika ƙokarin tsaftace cakuduwar Maza da Mata, a guraren maulidin da kuma kaucewa abubuwan da basu kamata ba.

 

‘Yan Sandan Zone One Sun Kama Wani Mutum Bisa Zarginsa da Damfarar Masu Neman Aiki ta Hanyar Kirkirar Takardun Ɗaukar Aiki na Bogi

The post Bai Kamata Malamai Su Dinga Kafurta Masu Yin Maulidi ba – Dan Azumi Gwarzo appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow