Al’ummar Unguwanni Goma Dake Jihar Bauchi Sun Koka Kan Yadda Kamfanin Lantarki na JED ke Gasa Musu Aya a Hannu

Daga Mu’azu Hardawa Bauchi.   Al’ummar wasu Unguwanni Goma da ke arewacin Jihar Bauchi, sun fusata game da abin da suka kira yaudara da tauye musu hakki da kamfanin samar da lantarki na Jos Electric Distribution (JED), ke yi a yankin tun tsawon shekaru sama da ashirin da suka gabata.   Unguwannin da suka yi […] The post Al’ummar Unguwanni Goma Dake Jihar Bauchi Sun Koka Kan Yadda Kamfanin Lantarki na JED ke Gasa Musu Aya a Hannu appeared first on GTR .

Al’ummar Unguwanni Goma Dake Jihar Bauchi Sun Koka Kan Yadda Kamfanin Lantarki na JED ke Gasa Musu Aya a Hannu












Daga Mu’azu Hardawa Bauchi.

 

Al’ummar wasu Unguwanni Goma da ke arewacin Jihar Bauchi, sun fusata game da abin da suka kira yaudara da tauye musu hakki da kamfanin samar da lantarki na Jos Electric Distribution (JED), ke yi a yankin tun tsawon shekaru sama da ashirin da suka gabata.

 

Unguwannin da suka yi wannan koke sun hadar da Madina kwatas, Gida dubu, Tafawa Balewa Estate, Bayan GG da wani fannin Dawaki da dai sauran su, inda suka baiyana takaicinsu game da cutar dasu da kamfanin JED ke yi a sakamakon yadda suke biyan kudin haske da kudin duhun da suke sha.

 

Sarkin Rano ya Tura Karin Hakimai Wasu Gundumomin da ke Ƙarkashin Masarautar

 

Da yake karin haske a yayin taron maneman labaran da ya jagoranci dandazon magidantan yankin a jiya Asabar, Malam Danlami Baban Takko, ya ce JED kamfanin lantarki ne na ‘Yan kasuwa, don haka bai dace ba kullum tunanin su shine su tatse mutane ta hanyar karɓar kudin aikin da ba’a yi musu ba.

 

A cewarsa, “Sama da shekara 20 tun ana zamanin NEPA ake gasa mana Aya a Hannu, wanda sai a kwashe makonni a wani yankin babu wutar awa guda amma karshen wata na yi za’a kawo takardar biyan kudi (Bill), kuma dole Mu biya ko a yanke. Kuma idan Maigida ya bari aka yanke haka za’a ci gaba da kawo takardar (Bill) ana masa lissafin bashin Matacce da Rayayye”.

 

Gwamnatina za ta Kara Hada Kai da Shugabannin Addinai Domin Inganta Zaman Lafiya da Hakuri da Juna – Tinubu

 

Yace sun bi duk wata hanyar maslaha sun yi tarurruka Kala-Kala sun kai kuka ofishin Kamfanin da sauran hukumomi amma lamarin ya zamo gobara daga Kogi, maganinta sai dai Allah.

 

Adan haka ne suka koma kiran ‘Yan jarida don baiyana bacin ran su, koh gwamnatin jihar Bauchi da hukumomin da suka dace za su kawo musu dauki, tunda sun fidda tsammani kan daidaituwar lamuran a tsakaninsu da JED.

 

Hukumar Alhazan Jihar Bauchi ta Sanar da Lokacin Fara Karɓar Kuɗin Aikin Hajjin Shekarar 2027

 

A nasa jawabin, Dakta Auwal Ibrahim, ya ce yanzu haka sun zamo saniyar tatsa a kamfanin JED biyo bayan yadda duk lokacin da suka kai kuka, sai an bukaci kudi a hannun su da nufin kawo ƙarshen siyen kayan da ake bukata don kawo karshen matsalar.

 

Shima Limamin masallacin Khalid bin Walid, Alhaji Anas Babajada, ya ce yanzu lamarin ya koma “Rashin ta Ido”, domin a halin yanzu sama da naira Milyan goma ake nema a hannun su don yin gyaran wasu abubuwan da an jima ana canza wa.

 

Al’ummar Garin Alhaji Tagidadu Sun yi Barazanar Kauracewa Zaben 2027 Saboda Rashin Sharbar Romon Demokradiyya

 

A karshe sun buƙaci gwamnatin jihar Bauchi da sauran hukumomi su shiga lamarin domin a bi musu hakkinsu, don kar alhakin ya Kama Kamfanin Lantarkin kamar yadda ya kama NITEL wayoyin hannu suka shigo suka kashe shi Murus.

 

‘Yan Sandan Jigawa Sun Kama Waɗanda Suke Zargi da Yunkurin Garkuwa da Mutane da Sauran Laifukan Daban-daban

The post Al’ummar Unguwanni Goma Dake Jihar Bauchi Sun Koka Kan Yadda Kamfanin Lantarki na JED ke Gasa Musu Aya a Hannu appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow