Al’ummar Fego na Ƙaramar Hukumar Alkaleri Sun Nemi Daukin Mahukuntan Jihar Bauchi Kan Dawowar ‘Yan Bindiga

Daga Mu’azu Hardawa Bauchi.   Al’ummar yankin Fego a Ruga mai kasuwa da ke kasar Gwana ta karamar hukumar Alkaleri, sun nemi ɗaukin mahukuntan jihar Bauchi da hukumomin tsaro, saboda mummunan hari da ‘yan bindiga suka kai musu a tsakiyar daren jiya Asabar.   Daya daga cikin jagororin yankin, Sheikh Yusuf Bello (Gafakan Ƙasar Gwana), […] The post Al’ummar Fego na Ƙaramar Hukumar Alkaleri Sun Nemi Daukin Mahukuntan Jihar Bauchi Kan Dawowar ‘Yan Bindiga appeared first on GTR .

Al’ummar Fego na Ƙaramar Hukumar Alkaleri Sun Nemi Daukin Mahukuntan Jihar Bauchi Kan Dawowar ‘Yan Bindiga












Daga Mu’azu Hardawa Bauchi.

 

Al’ummar yankin Fego a Ruga mai kasuwa da ke kasar Gwana ta karamar hukumar Alkaleri, sun nemi ɗaukin mahukuntan jihar Bauchi da hukumomin tsaro, saboda mummunan hari da ‘yan bindiga suka kai musu a tsakiyar daren jiya Asabar.

 

Daya daga cikin jagororin yankin, Sheikh Yusuf Bello (Gafakan Ƙasar Gwana), ne ya bukaci hakan a madadin dubun dubatar al’ummar, a zantawarsa da GTR Hausa, inda ya ce ‘Yan bindiga sun kawo harin ne kamar yadda suka yi ta kawowa a watannin baya, har suka tarwatsa yankin, lamarin da ya tilasta wa mutane yin hijira zuwa jihar Gombe da wasu garuruwa don tsira da rayukan su.

 

‘Yan Bindiga Sun yi Garkuwa da Alƙalin Babbar Kotun Jihar Kebbi

 

Wanda kuma bayan daukar tsauraran matakai daga gwamnatin jihar Bauchi da hukumomin tsaro an samu lafawar matsalar, har mutane sun koma yankunan su na asali tare da fara noma gonakin su, sai dai kuma a daren wannan Asabar maharan suka sake fitowa dauke da manyan Makamai tare da afka wa garin Ruga Maikasuwa, inda suka raunata mutane shida waɗanda a halin yanzu suke Asibitin jihar Gombe.

 

Bugu da kari ya ce Maharan sun kwashe shanun noma da kaya masu muhimmanci, wanda ake ci-gaba da bincike don sanin ko sun tafi da mutane. Amma kasancewar mutanen yankin sun yi jarumtar maida martani a cikin daren wanda ya tilasta wa maharan guduwa da iya dabbobin da suka iya korawa.

 

Babbar Kotun Taraiya ta Gargaɗi ACP Babagana na Zone One Kano, Kan Ƙin Bin Umarnin ta

 

Adan haka Sheikh Yusuf ya bukaci gwamnati ta kawo musu dauki ta hanyar samar da rundunar Soji a yankin mai makwbtaka da jihohi biyar da manyan gandun daji irin su Yankari da makamantan su, wuraren da ‘Yan bindiga ke samun mafaka.

 

Wakilin GTR Hausa a jihar Bauchi, Mu’azu Hardawa, ya tuntubi Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Nafiu Habib, inda ya ce bai sami labarin ba amma zai kira Baturen ‘Yan Sanda (DPO) na Alkaleri don jin ta bakin sa, harma ya ce za su ɗauki matakin tura karin Jami’an tsaro don su dauki matakin da ya dace na kare mutane domin su ci-gaba da zama a garuruwan su.

 

Duk Al’ummar da ta Fifita Kudi Akan Mutunci, Toh ta Kauce Hanyar Gaskiya – Ambasada Gashash

The post Al’ummar Fego na Ƙaramar Hukumar Alkaleri Sun Nemi Daukin Mahukuntan Jihar Bauchi Kan Dawowar ‘Yan Bindiga appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow