Akwai Damuwa Kan Tsarin Tarbiyya da Zamantakewar Dalibai A Makarantun Jihar Bauchi – Kwamishinan Ilimi

Daga Mu’azu Hardawa Bauchi.   Kwamishinan Ilimi na Jihar Bauchi, Alhaji Abdulkadir Ibrahim, ya ce akwai matuƙar damuwa kan tsarin tarbiyya da zamantakewar dalibai a makarantun jihar.   Abdulkadir ya bayyana hakan ne a yayin zantawarsa da manema labarai, jim kaɗan bayan rangadin da ya kai wasu makarantun gwamnati da ke jihar, don duba yadda […] The post Akwai Damuwa Kan Tsarin Tarbiyya da Zamantakewar Dalibai A Makarantun Jihar Bauchi – Kwamishinan Ilimi appeared first on GTR .

Akwai Damuwa Kan Tsarin Tarbiyya da Zamantakewar Dalibai A Makarantun Jihar Bauchi – Kwamishinan Ilimi












Daga Mu’azu Hardawa Bauchi.

 

Kwamishinan Ilimi na Jihar Bauchi, Alhaji Abdulkadir Ibrahim, ya ce akwai matuƙar damuwa kan tsarin tarbiyya da zamantakewar dalibai a makarantun jihar.

 

Abdulkadir ya bayyana hakan ne a yayin zantawarsa da manema labarai, jim kaɗan bayan rangadin da ya kai wasu makarantun gwamnati da ke jihar, don duba yadda ake gudanar da jarrabawar NECO da kuma zamantakewar daliban makarantun.

 

Hotuna: Yadda CP Omolori ya Ziyarci Garin Azare Kan Rikicin da ya Faru a Tsakanin Kungiyoyin Matasa

 

A cewarsa, “Raba ɗalibai maza da mata a makarantu kaɗai ba zai magance matsalar tarbiyya ba, domin tarbiyyar yara nauyi ne da ya rataya a kan iyaye, makaranta da kuma al’umma baki ɗaya, tunda idan an raba daliban a makaranta, ai ba za a raba su a gida ko a waje ba”.

 

Ya ce tsarin da ya mayar da wasu makarantu na maza kaɗai ya haifar da matsalar ƙarancin amfani da kayan more ilimi da gwamnati ta samar, inda ya ce Ajuzuwa da dama sun kasance babu ɗalibai.

 

Muhammad ya Sake Zama Sunan da Aka fi Sanya wa Jarirai a Ingila da Wales

 

Ya kuma bayyana cewa wasu iyaye sun janye ‘ya’yansu daga makarantun saboda rashin damar tura su zuwa makarantu masu nisa, musamman a wannan lokaci na matsin tattalin arziki duba da yadda suke ƙoƙarin neman abincin da za su rufawa kansu da iyalansu asiri.

 

A shekarun baya ne dai tsohon kwamishinan ilimi na jihar, Dakta Aliyu Tilde, ya fito da sabon tsarin raba makarantun Sakandire inda suka kasance na Maza daban na Mata daban, har ma da tsarin yin jarrabawa kafin a kai dalibai makarantun kwana, lamarin da ya haifar da dukkan makarantun kwana suka rasa dalibai, baya ga yadda mafi yawancin makarantun da suke da dubban Dalibai suka koma masu daruruwa.

 

APC ta Tabbatar da Kashim Shettima a Matsayin Abokin Takarar Tinubu a Zaben 2027

The post Akwai Damuwa Kan Tsarin Tarbiyya da Zamantakewar Dalibai A Makarantun Jihar Bauchi – Kwamishinan Ilimi appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow