A Guji Tsundama Addini a Siyasa – Ministan Tsaron Najeriya

Daga Kallamu Galadima Dambo.   Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Gwabin Musa, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su ƙara ƙarfafa haƙurin addini, haɗin kan ƙasa da zaman lafiya dorewa a tsakaninsu, yana mai cewa kyakykyawar mu’amala tsakanin mabiya addinai da ƙabilu daban-daban na da matuƙar muhimmanci wajen gina Najeriya da ci-gaban kasa.   […] The post A Guji Tsundama Addini a Siyasa – Ministan Tsaron Najeriya appeared first on GTR .

A Guji Tsundama Addini a Siyasa – Ministan Tsaron Najeriya












Daga Kallamu Galadima Dambo.

 

Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Gwabin Musa, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su ƙara ƙarfafa haƙurin addini, haɗin kan ƙasa da zaman lafiya dorewa a tsakaninsu, yana mai cewa kyakykyawar mu’amala tsakanin mabiya addinai da ƙabilu daban-daban na da matuƙar muhimmanci wajen gina Najeriya da ci-gaban kasa.

 

Ba Zamu Dawo da Tallafin Man Fetur ba – Fadar Shugaban Najeriya

 

Ministan ya baiyana hakan ne a jihar Kaduna, a lokacin da yake ganawa da masu kula da tsarin GG Musa 4 PBAT 2027, wato ƙungiyar da ya kafa domin wayar da kan jama’a da tattara masu zaɓe don nuna goyon baya ga Shugaba Tinubu da Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani, a babban zaɓen 2027.

 

A Guji Tsundama Addini a Siyasa - Ministan Tsaron Najeriya 

 

A gefe guda suma ‘yan siyasan yn hore su da su kasance masu nisanta kalamansu da duk wani abu da zai baiwa ‘yan Adawa damar shigar da wata suka mai alaka da addini, yare ko nuna bangaranci a tsakanin ‘yan Najeriya.

 

Gwamnatin Zamfara ta Ƙara wa Ɗalibai Hutun Makaranta na Sati Biyu

 

Tuni dai jagororin addinai a Najeriya ke ci-gaba da kira ga ‘yan kasar domin ganin sun guji karkatar da maganganun ‘yan siyasa da nufin cimma wata manufa ta Ƙashin Kai.

 

Taron ya sami halartar shugabannin ƙungiyar, masu kula da harkokinta daga ƙananan hukumomi 23 na Jihar Kaduna, da kuma wakilan ƙungiyoyin tallafa wa siyasa da sauran masu ruwa da tsaki sama da 300 da ke ƙarƙashin tsarin.

 

Dokar Wa’azi Wajibi ce a Najeriya – Nasiru Salisu Zango

The post A Guji Tsundama Addini a Siyasa – Ministan Tsaron Najeriya appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow