Ƙungiyar ‘Yan Kasuwar Arewa Tayi Alkawarin Horas da Mambobinta Dabarun Kasuwancin Zamani

Daga Kallamu Galadima Dambo.   Kungiyar ‘Yan Kasuwar Arewa (Arewa Traders Association), ta sha alwashin horas da mambobinta dabarun kasuwanci na Zamani.   Shugaban kungiyar na Kasa, Alhaji Adamu Hassan, ne ya baiyana hakan a yayin taron da kungiyar ta shiryawa Mambobinta a babban birnin tarayya Abuja, inda ya ce taron na haɗin guiwa ne […] The post Ƙungiyar ‘Yan Kasuwar Arewa Tayi Alkawarin Horas da Mambobinta Dabarun Kasuwancin Zamani appeared first on GTR .

Ƙungiyar ‘Yan Kasuwar Arewa Tayi Alkawarin Horas da Mambobinta Dabarun Kasuwancin Zamani












Daga Kallamu Galadima Dambo.

 

Kungiyar ‘Yan Kasuwar Arewa (Arewa Traders Association), ta sha alwashin horas da mambobinta dabarun kasuwanci na Zamani.

 

Shugaban kungiyar na Kasa, Alhaji Adamu Hassan, ne ya baiyana hakan a yayin taron da kungiyar ta shiryawa Mambobinta a babban birnin tarayya Abuja, inda ya ce taron na haɗin guiwa ne tsakaninsu da Bankin Jaiz da kuma TajBank.

 

Kotu ta Ci-gaba da Sauraron Shari’ar Zaben Fidda Gwanin Kujerar Gwamnan Jihar Nasarawa na Jam’iyyar ADC

 

A cewarsa, “Manufar haduwar ‘yan kasuwar shine bada horo kan dabarun kasuwanci na zamani domin kar a bar su a baya”.

 

Ƙungiyar 'Yan Kasuwar Arewa Tayi Alkawarin Horas da Mambobinta Dabarun Kasuwancin Zamani

 

Ya kuma buƙaci gwamnatin Najeriya da na jihohin kasar dasu duba buƙatun da suka dade suna nema a garesu, musamman duba da irin gudunmuwa da suke bayarwa ga gwamnati dama al’ummar kasa baki daya.

 

Shugaba Tinubu ya Fadada Rundunonin Sojin Kasa Zuwa Rukuni 12 Tare da Daukar Sabbin Sojoji 28,000

 

Yusif Kabir, shine ya wakilci Bankin Taj a wajen taron, ya ce sun yi farin ciki da shirya wannan taro wanda ya ce zai taka rawa wajen tattauna hanyoyin ci-gaban kasuwanci da kuma nemo hanyoyin magance matsalolin da fannin ke fuskanta.

 

Shima Jibrin da ke a matsayin ma’aikacin Bankin Jaiz, ya ce manufar shirya taron shine domin kara faiyace wa ‘yan kasuwa tsarin kasuwanci a Musulunce da tsarin da addinin ya tanadar domin mutane su amfana.

 

PCACC Kano ta Dakatar da Yunƙurin Gina Gidaje da Rushe Gidajen Malamai a Makarantar ’Yan Mata ta WTC

 

A ƙarshe Zainab Abdulfatai da Umar Sheikh Isma’il, da ke cikin mahalarta taron na yini guda sun ce babu shakka zai taimaki kasuwancinsu ta fuskoki da dama wajen bunƙasa ribar su da kuma hanyar karin samun kudaden shiga.

 

Taron ya gudana ne a yau Alhamis, 23 ga watan Yulin shekarar 2026, a dakin taro na Women Development Center da ke Abuja, inda ya sami halartar ‘yan kasuwa daga sassa daban-daban na Najeriya.

 

Kotu ta Yanke wa Mutanen da ta Samu da Laifi a Sace Ɗaliban Jihar Oyo Hukuncin Ɗaurin Rai da Rai

The post Ƙungiyar ‘Yan Kasuwar Arewa Tayi Alkawarin Horas da Mambobinta Dabarun Kasuwancin Zamani appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow